Kungiyar kwadago ta janye shiga yajin aiki, gwamnati za ta biya N30,000

LABARAI DAGA 24BLOG
[Post by samaila umar lameedo]
Bayan tafka doguwar muhawa, jaridar Vanguard, ta ruwaito cewa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa don kawo maslaha kan batun karin albashi mafi karanci ga ma'aikata, ya amince da bukatar kungiyar kwadago, na maida albashi mafi karancin zuwa N30,000.
A karshen zaman farko da kungiyoyin kwadagon da kwamitin suka gudanar, sun cimma matsaya daya kan yadda tsarin karin albashin zai kasance, shugabar kwamitin wacce kuma ita ce tsohuwar shugabar ma'aikata ta kasa, Ms Ama People, ta ce a lokacin da gwamnati na tsaya kan N24,000 su kuma kungiyoyin kwadagon sun ja tunga akan N30,000.
Da dumi dumi: Kungiyar kwadago ta janye yajin aikin da ta shirya shiga 6 ga Nuwamba
"Mun cimma matsaya a yanzu, sai dai muna da yan gyare gyare da zamu yi a sashe na biyar na rahotonmu, sashen da muke dauke da kididdigar kudaden kamar yadda kowa ya gabatar. A yanzu, kwamitin zai gabatarwa gwamnatin tarayya, ta zaba tsakanin N24,000 ko N30,000.
"Mun kammala komai yanzu, sai dai mun roke su, akan su hakura su janye wannan kudiri na su na shiga yajin aikin," a cewar Ms People.
Dangane da sanin ko za a ci gaba da bin umurnin Kungiyar kwadago na shiga yajin aiki, majiya daga kungiyoyin kwadagon ya ce a'a, da alamar sanarwa ga sauran shuwagabannin kungiyoyin kwadago.
Sai dai gaba daya shuwagabannin kungiyoyin kwadagon da suka halarci taron, sun ki zanatawa da manema labarai, suna masu cewa sun fito hutun gajeren lokaci ne, za su koma a cikin daren don ci gaba da tattaunawa.