Kun san garin da yara ke makancewa a Abuja

LABARAI DAGA 24BLOG
[post by samaila umar lameedo]
Ruga wani yanki ne a wajen babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da sama da mutum 10,000 ke zaune a yankin. Mutanen suna fama da matsalolin rashin ruwa da kuma fama da wasu cutuka.
Rashin ingantaccen ruwa sha shi ne babbar matsalar yankin na Ruga, sai kuma matsalar rashin bandakai da rashin tsaftar muhalli.
Matsalolin suna haifar da cututtuka musamman ma makanta ga kananan yara, wacce take naksa su tun suna kanana.