[post by samaila umar lameedo]
Ku kamo mana Oshiomhole ku dawo dashi Najeriya - PDP ga Interpol

LABARAI DAGA 24BLOG
- Jam'iyyar adawa ta PDP tayi kira ga INTERPOL da NIA dasu nemo Adams Oshiomhole
- Barin shi kasar a yayin da ake tsaka da bincike akan shi na iya bada tabbacin aikata laifin
- Dama shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke kare shi daga hukunci domin kare mutuncin jam'iyyar APC, inji PDP
Ku kamo mana Oshiomhole ku dawo dashi Najeriya - PDP ga Interpol
Jam'iyyar adawa ta PDP tayi kira ga INTERPOL da NIA dasu nemo shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.
Barin kasar a yayin bincike zai iya sa a zarge shi ko a tabbatar da zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke kare shi daga fuskantar hukunci domin kare jam'iyyar APC, inji PDP.
A kalaman mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yace:
"Abin mamaki ne ace, a cikin karairayin APC, sun yarda cewa Idan suka hana kama Oshiomhole da kuma taimaka mishi gurin barin kasar zasu yi nasara gurin gujewa DSS da kuma batar da hankalin mutane.
Yan Najeriya sun san cewa, Oshiomhole bai musa zargin da ake mishi ba, ya kuma sanar cewa shugabancin kasa ta aminta da duk abinda yayi."
Jam'iyyar adawar ta kwabi Oshiomhole akan 'girman kai, son mulki ido rufe da kuma watanda da dukiyar al'umma'.
Tace in har ansan ya ci rashawa, gara kawai a bar shi ya fuskanci shari'a tare da aje mukamin sh