[post by samaila umar lameedo]

Kano: Kun san Kiristocin da ke kai kara wajen 'yan Hisbah?

Dis Nigerian Christians for Kano no see anything wrong to take dia problem to Islamic police
Image captionWadannan mabiya addinin Kirista a Kano ba sa ganin aibin kai kara zuwa wajen 'yan Hisbah
Wasu mabiya addinin Kirista a Kano a Najeriya sun ce sun fi jin dadin kai kokensu zuwa wajen 'yan Hisbah da kotunan Musulunci maimakon zuwa wajen 'yan sanda.
Komolafe Johnson wanda shi ne shugaban wata kungiyar Kiristoci mai suna 'Humanity Peace and Leadership Synergy Initiative' a Sabon Garin Kano, ne ya shaida wa BBC haka.
Ya ce: "Jami'an Hisbah ba sa karbar kwabo a hannunka kuma su kan tabbatar da an warware matsalar da ka kai wurinsu .
"Ba da dadewa ba muka kai wata kara tsakanin wani mai gidan haya Musulmi da dan haya Kirista, kuma sun sasanta su.
"Abin mamakin shi ne sun rika karanto wasu ayoyi daga littafin Babul a lokacin da ake sauraron karar", in ji Mista Johnson.
Ya kuma ce shekaru da dama kenan yana kai kara zuwa wurin hukumar ta Hisbah kuma a duk tsawon wannan lokacin ba su taba karbar ko kwabo a wurinsa ba.
Komolafe Johnson
Image captionMista Komolafe Johnson
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya ke kusantar hukumar ta Hisbah, duk da cewa yawancin Kiritocin da ke Kano na tsoron jami'anta, sai Johnson ya ce a lokacin da aka yi zanga-zangar karin kudin mai a shekarar 2011 wanda ya janyo mummunar tashin hankali, 'yan Hisbah ne suka rika raka su zuwa coci kuma suka rika gadinsu hara bayan sun kammala ibadar da suka je yi.
"Wannan taimakon da suka yi mana ne ya sa na gane cewa mutanen kirki ne ba kamar yadda wasu mutane ke masu mummunar fahimta ba."
Mista Johnson ya kara da cewa idan dai yana da sauran rai a jikinsa, kuma ya ci gaba da zama a Kano, to kungiyarsa ba za ta fasa kai dukkan matsalolin da suka dame su wajen hukumar ta Hisbah ba.
Ya ce "Miyagun halayen da Hisbah ke kokarin hanawa kamar shan giya da karuwanci sun yi daidai da abin da littafinmu na Baibul ya hana, ka ga kenan suna taimakawa Kiristoci da sauran al'umma matuka."
Dis Nigerian Christians for Kano no see anything wrong to take dia problem to islamic police
Kakakin Hukumar Hisbah, Adamu Yahaya ya ce wannan matakin da wadannan Kiristocin ke dauka ya nuna cewa ba dukkansu ne ke adawa da dokokin Musulunci da ayyukan Hisbah ba.
"Muna hada kai da wannan kungiyar sosai domin su kan kawo mana matsalolinsu domin mu taimaka a warware su.
"Suna kuma gayyatar mu zuwa wasu daga cikin bukukuwansu, kuma mu ma muna gayyatarsu zuwa namu."
Amma sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN reshen jihar Kano, Ibrahim Isa Wangida ya ce kungiyarsu ba ta amince da wanna tsarin ba, domin Kiristocin da ke kai kara wajen Hisbah ba za su yarda da hukuncin Hisban ba idan Musulmi suka kai su kara can.
"A ganinmu wannan ba ingantaccen tsari ne ba domin wadannan Kiristocin da ke kai kara zuwa wurin Hisbah a maimakon zuwa wurin 'yan sandan gwamnati na iya kin amincewa idan wasu suka kai su kara wajen 'yan Hisbah."
Amma Wangida ya ce suna da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da Hisbah, kuma ba da dadewa ba da wasu yara Kirista suka bata, hukumar Hisbah ce ta gano su kuma ta mika su ga kungiyar CAN kafin daga baya aka mika su ga iyayensu.
A matsayinsa na lauya, ya bayyana cewa kamata ya yi a fayyace sassan da hukumar ta Hisbah ke da iko a cikin dokar shekara ta 2000 da ta kafa hukumar.
"A misali, Kiristoci sun fi yawa a yankin Sabon Garin Kano, kuma bai kamata su rika shiga can suna kwace giya da korar mutane daga otel-otel ba.
"Kana duk Kiristan da ke Kano na da ikon tafiyar da rayuwarsa ta yadda ya ga dama domin Hisbah ta Musulmi ce," in ji shi