[post by samaila umar lameedo]
Jam'iyyar UPP za ta mara wa Buhari baya

LABARAI DAGA 24BLOG
A yayin da al'amuran siyasa ke ci gaba da kankama a Najeriya, daya daga cikin jam'iyyun adawa da ake ganin tana da matukar tasiri a kudu maso gabashin kasar wato UPP, ta bayyana goyon bayanta ga jam'iyya mai mulkin kasar APC a zaben shugaban kasa da za a yi a badi.
Shugaban Jam'iyyar, Chekwas Okorie, ya ce sun mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya ne domin sun yi amanna cewa shi ne kadai zai iya share musu hawaye.
Mista Okorie, ya ce shekara 16 yanzu an mayar da su saniyar ware a harkokin siyasar kasar, hakazalika ya yi watsi da rade-radin da ke cewa suna bayan dan takarar Jam'iyyar adawa wato Atiku Abubakar.
A kwanakin baya an rinka samun tufka da warwara dangane da goyon bayan al'ummar yankin ga dan takarar shugaban kasa na PDPn, wanda ya zabo abokin tafiyarsa Peter Obi daga yankin.
Wanne dan takara Rahama Sadau za ta zaba tsakanin Atiku da Buhari?
Buhari da Atiku sun raba kawunan yan Kannywood
Me ya sa gwamnatin Buhari ke so mata su yi tazarar haihuwa?
Masu lura da lamuran siyasa na gani cewa wannan gagarumin ci gaba ne da Jam'iyyar APC ta samu musamman daga yankin kudu maso gabashin kasar, wato tushen ita jam'iyyar UPP.
Kusan a yanzu ana iya cewa jam'iyyar APC da dan takararta na fuskantar babban hamayya da suka daga yankin kudu maso gabashi, ko a shekara ta 2015 APC ba ta taka rawar gani ba a wadanan yankunan.
Sai dai kuma ana ganin goyon-bayan da UPP ta nuna wa APC ya yi tasiri, musamman a wannan lokaci da Jam'iyyar PDP da dan takararta na Shugaban kasa Atiku Abubakar ke samun gagarumin goyon baya daga al'ummar yankin.