Hukumar zabe ta INEC ta kammala amsar sunayen takarar zabukan 2019

LABARAI DAGA 24BLOG
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta rufe karbar sunayen 'yan takarar gwamnoni da 'yan majalisun jiha a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.
Babban daraktan yada labarai na hukumar Mista Oluwole Osaze Uzzi shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilin majiyar mu na kamfanin dillacin labarai a hedikwatar hukumar a garin Abuja.
Kurunkus: Hukumar zabe ta INEC ta kammala amsar sunayen takarar zabukan 2019
Hukumar zaben dai a kwanan baya ta fitar da sunayen 'yan takarar shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa daya daga cikin mutane 50 da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta hana fita ya sulale ya fice zuwa kasar Jamus.
Wanda ya fita din dai shine Orji Uzor Kalu dake zaman tsohon gwamnan Abiya kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC.