[post by samaila umar lameedo]
Hotunan shugaba Buhari a wurin taron kasashen gefen tekun Chadi

LABARAI DAGA 24BLOG
A jiya, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa N'Dajamena, babban birnin kasar Chadi, domin shugabantar taron shugabannin kasashen Afrika dake da makwabtaka da tekun Chadi (LBC).
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar Buhari ya yi amfani da matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen wajen kiran taron domin tattauna yadda za a samu zama zaman lafiya mai dorewa a rukunin kasashen LBC dake fama da hare-haren 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.
A wata sanarwa da Femi Adesina, karamin kakakin shugaba Buhari, ya fitar a Abuja ya ce za a yi taron ne yau, Alhamis, a N'Dajamena.
Shugaba Buhari bayan ya isa N'Djamena domin taron shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

shugaba Buhari tare da shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

Shugaba Buhari tare da shugabannin kasashen gefen tekun Chadi
Adesina ya bayyana cewar an gayyaci shugaban kasar Benin zuwa wurin taron saboda kasar sa ta bayar da gudunmawar sojoji domin yakar aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.
A cewar Adesina, taron na kwana daya zai tattauna yanayin tsaro a tsakanin kasashen da niyyar samar da hanyoyin da za a bi domin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram.