[post by samaila umar lameedo]
Gwamnatin Obama ta yi min katsalandan a 2015 — Jonathan

LABARAI DAGA 24BLOG
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya wuce gona da irin kan yadda ya yi katsalandan a zaben shugaban kasa na Najeriya a 2015, wanda Jonathan din bai yi nasara ba.
Gabanin zaben dai Shugaba Obama ya fitar da wani bidiyo yana yi wa 'yan Najeriya magana kan zaben, sannan kuma ya aike da sakataren sa na harkokin kasashen waje John Kerry zuwa Najeriya, bayan dage zaben kasar daga watan Fabrairu zuwa Maris saboda dalilan tsaro.
"Irin yadda gwamnatin Obama ta yi mana katsalandan abin ya wuce kima," inji Jonathan.
Jonathan bai fadi gaskiya ba kan sace 'yan matan Chibok —Shettima
Ni ne wanda aka fi suka a duniya — Jonathan
Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC, kan wasu batutuwa da ke cikin littafinsa
My Transition Hours da aka kaddamar a Abuja.
Tsohon shugaban ya shaidawa BBC cewa ya damu kan yadda zaben shekarar 2019 zai gudana, musamman ma irin rawar da hukumomin gwamnati za su taka a zaben.
Jonathan ya ce mutane da dama a ciki da wajen Najeriya sun damu da irin rawar da hukumar zaben kasar INEC da hukumomin tsaro za su taka, sai dai ya ce yana da yakini za su yi abinda ya kamata.
Dangane da zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin sa kan sakaci wajen sace 'yan matan Chibok kuwa, da rashin yunkurin gano su a kan kari, Goodluck ya ce ba zai duaki alhakin abinda ya faru ba.
Yace Boko Haram gaggan masu laifi ne. "A matsayi na na shugaban kasa ba ni ne zan je filin yaki ba, akwai jami'an tsaro da ke tattara bayanan sirri wandanda suke aikin su."
Ya kara da cewa jami'an tsaron sun kokarta, sai dai yunkurin da suka yi bai isa ya kai ga cewa an ceto 'yan matan ba.
Tsohon shugaban na Najeriya wanda ya yi mulki daga shekarar 2010 zuwa ta 2014 ya ce ya gudanar da gwamnati cikin wani mawuyacin hali. Abubuwa da dama sun taso a lokacin, a cewarsa.
"Kamar batun cire tallafin mai da batun sace 'yan matan Chibok da wasu batutuwan da suka ringa janyo ce-ce ku ce.
Dangane da batun asusun Najeriya kuwa da ake zagin gwamnatin sa ta bar shi fanko, Jonathan ya ce, ai kuwa idan ba a yabe shi ba a a kushe masa ba.
Ya ce saboda yadda ya ringa kokarin alkinta kudin kasar da ke asusun kasahen waje, har kotu gwamnonin kasar suka kai shi kan cewa sai an rabe kudin baki daya.