Duba wasu romon dimukradiyya 5 da Sakkatawa suka sharba daga gwamnatin Buhari

LABARAI DAGA 24BLOG
Bukatar maje Hajji sallah, Inji masu iya magana, haka zalika a duk inda aka ce harkar siyasa ta shiga tsakanin wasu mutane, toh tabbas harkace irin ta bukata, inda bangarorin biyu ko fiye da haka zasu yi yarjejeniya akan afmanin da zasu samu da juna, haka ake yi a siyasun da suka cigaba.
Sai dai anan Najeriya ba kasafai ake samun ire iren wadannan yarjejeniya ko alkawurra tsakanin yan siyasa da jama’a ba, musamman idan dan siyasan nan Muhammadu Buhari ne, wanda ya kwashe tsawon shekaru goma sha shida yana tsayawa takarar shugaban kasa sakamakon kaunarsa da ta mamaye zuciyan talakan Arewa.
Sokoto
Amma duk da cewa ba’a samu ire iren alkawurran tsakaninsa da jama’a kai tsaye ba, amma ya dauki wasu muhimman alkawurra guda uku, sune; tabbatar da tsaro, saita tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, wadannan sune alkawurran da yake ambata a duk inda yaje yakin neman zabe a 2015.
Sai dai a kokarinsa na cika alkawurran nan, Buhari bai manta da jahar Sakkwato ba, Sakkwato birnin Shehu, Jahar da ya samu kuri’u dubu dari shida da saba’in da daya, da dari tara da ashrin da shida (671,926) a zaben 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Sokoto
Yayin da shugaban kasa a wancan lokaci, Goodluck Jonathan ya samu kuri’u dubu dari da hamsin da biyu, da dari daya da casa’in da tara (152,199) a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, wanda hakan ya baiwa Buhari daman lashe zaben da kuri’un da suka haura miliyan 15, yayin da Jonathan ke da miliyan 12.
Don haka idan aka duba da gudunmuwar da al’ummar jahar Sakkwato ta bayar ga shugaba Buhari, ya zama wajibi shugaban ya tuna da ita a duk lokacin da aka shiga fagen sharbar romon dimukradiyya. Ga wasu daga cikin ayyukan da mora, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.
- Aikin gyaran hanyar da ta tashi daga Sakkwato-Tambuwal- Jega, kasha na daya
- Aikin gina sabbin gadoji a Mayanchi, kan iyakar Gusau da Sakkwato
- Aikin gina gidajen gwamnatin tarayya masu dakuna 2, 3 da ma 1
- Aikin gyaran hanyar Sakkwato zuwa Ilela
- Daukan ma’aikatan N-Power, akalla dubu goma da dari takwas da sittin da biyar (10, 865)