Daya daga wadanda Buhari ya hana fita kasar waje ya sulale ya tafi kasar Jamus

LABARAI DAGA 24BLOG
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa daya daga cikin mutane 50 da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta hana fita ya sulale ya fice zuwa kasar Jamus.
Wanda ya fita din dai shine Orji Uzor Kalu dake zaman tsohon gwamnan Abiya kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC.
Daya daga wadanda Buhari ya hana fita kasar waje ya sulale ya tafi kasar Jamus
Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Kunle Oyewunmi ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya fita ne tare da matar sa, Ifunanya a ranar Litinin din da ta gabata.
Sai dai rahotannin da muke samu na nuni ne da cewa motar marasa lafiya ne ta dauki tsohon gwamnan zuwa wata asibiti mai suna Helios Klinik a can Jamus din.
A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta rufe karbar sunayen 'yan takarar gwamnoni da 'yan majalisun jiha a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.
Babban daraktan yada labarai na hukumar Mista Oluwole Osaze Uzzi shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilin majiyar mu na kamfanin dillacin labarai a hedikwatar hukumar a garin Abuja.