[post by samaila umar lameedo]
Buhari ya jagoranci rantsar da shugaba da kwamishinonin FCSC (hotuna)

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron rantsar da shugaba da kwamishinonin hukumar daukar ma’aikatan tarayya wato Federal Civil Service Commission (FCSC) a fadar shugaban kasa a Abuja a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba.
Legit.ng ta tattaro cewa mataimakin shugaban kasa na musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba.
Dr Yakubu Bello Ingawa aka rantsar a matsayin shugaban hukumar, yayinda aka rantsar da Cif Ejoh Michael Chukwuemeka a matsayin daya daga cikin kwamishinonin hukumar.
Ga hotunan taron a kasa: