Online counter

Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su yi koyi da Jonathan.

[post by samaila umar lameedo]
Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su yi koyi da Jonathan

LABARAI DAGA 24BLOG 
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan kasar su yi koyi da halaye irin na tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.
"Shugaba Buhari ya yi amannar cewa irin rayuwar da tsohon shugaban ya gudanar abar koyi ce ga dukkan matasan kasar," in ji sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina ya fitar.
Ya fitar da sanarwar ce a ranar Talata domin taya tsohon shugaban murnar cika shekara 61 a duniya.
Shugaba Buhari ya kara da cewa rayuwar Goodluck Jonathan ta kasance izina ga "dukkan mutumin da ke son ya yi koyi, ya yi aiki tukuru sannan ya sanya hannu wajen gina kasa ta gari."
Har ila yau, ya taya tsohon shugaban kasar murna game da kaddamar da littafin da ya rubuta kan yadda ya tafiyar da mulkin Najeriya.
Jonathan ya soki Buhari kan Zakzaky
Barayi 'sun wawashe' gidan Goodluck Jonathan na Abuja
Ranar Talata tsohon shugaban kasar ke kaddamar da littafin mai suna, My Transition Hours, don haka ne Shugaba Buhari ya yi kira ga 'yan kasar su koyi da Mr Jonathan wajen rubuta irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban Najeriya.
Shugaba Buhari da tsohon shugaban kasar cif Olusegun Obasanjo na cikin mutanen da Mr Jonathan ya gayyata wurin kaddamar da littafin.
Goodluck Jonathan dai ya mika mulki a hannu Shugaba Buhari bayan ya kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2015, abin da bai taba faruwa ba a tarihin kasar.
Amincewa da shan kayen da Mr Jonathan ya yi ya sa manyan kasashen duniya, ciki har da Amurka sun yaba masa.
Shi kansa Shugaba Buhari ya sha yaba wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kan amincewa da shan kayen da ya yi da kuma mika masa mulki ba tare da zubar da jini ba.
Sai dai Shugaba Buhari bai fasa caccakar tsoffin shugaban kasar ba, ciki har da Mr Jonathan, kan abin da ya kira "lalata kasar da kuma rashin aiwatar da ayyukan da suka dace duk da dimbin kudin da suka samu lokacin da suke kan mulki."

Post a comment

0 Comments