[post by samaila umar lameedo]

Biri ya kashe wani jariri a Indiya

  • Sa'o'i 9 da suka wuce
Birrai a Indiya na fuskantar matsin lamba daga wajen mutaneHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBirrai a Indiya na fuskantar matsin lamba daga wajen mutane
Wani jariri mai kwana 12 a duniya ya rasu bayan da wani biri ya kwace shi daga hannun mahaifiyarsa kuma ya cije shi a arewacin Indiya.
Iyalinsa sun ce mahaifiyar na shayar da jaririn a gidansu da ke birnin Agra ne lokacin da daban ya shiga gidan ya kwace shi.
Bayan da birin ya ciji jaririn sai ya ajiye shi a kan rufin kwanon gidan makwabtansu a yayin da mazauna garin suka bi dabban.
Jaririn ya rasu a asibiti sakamakon raunukan da ya ji. Mazauna garin sun ce hare-haren da birrai su ke kai wa yankin na karuwa sosai.
Kawun jaririn, Dhirendra Kumar, ya shaida wa BBC cewa dangin jaririn na cikin dimuwa.
Ya kara da cewa: "Akwai birrai da dama a yankin. Muna rayuwa cikin tsoro. Mun gaya wa hukuma sau da dama cewa su taimaka mana, amma har yanzu babu abunda suka yi.
"Mahaifiyar jaririn na cikin dimuwar da ba ma ta iya magana saboda halin takaici da ta ke ciki," in ji shi.
Pushpa Devi, kakar jaririn ta ce iyalan ba za su taba mantawa da wannan abu ba.
Pushpa Devi, kakar jaririn, ta shaida wa BBC cewa mutane na rayuwa a cikin jin tsoroHakkin mallakar hotoYOGESH KUMAR SINGH
Image captionPushpa Devi, kakar jaririn, ta shaida wa BBC cewa mutane na rayuwa a cikin jin tsoro
Ta kara ta cewa: "Na rasa jikana. Sa'o'i kadan kafin birin ya kai hari kan jaririn, ina dauke da shi.
"Bai kamata jaririnmu ya rasu ba. Mutane za su yi ta maganar na kankanin lokaci sai su manta. Amma dole mu yadda cewa jaririnmu ya tafi har abada."
Ajay Kaushal, jami'in da ke kula da ofishin 'yan sanda da ke kusa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an ji wa jariri munanan raunuka.
Ya kara da cewa: "Birin ya ciji kan jaririn, sai kuma ya ajiye shi saboda mazauna garin sun bi shi da itatuwa kuma suna jifan shi da duwasu."
Harin na baya-bayan nan na cikin jerin hare-hare da birrai kan kai a Agra, wurin da ke kusa da Fadar Taj Mahal, wanda ya fi kowane wuri shahara a tarihin Indiya.
Watanni biyu da suka wuce, birrai sun kai wa wani karamin yaro hari kuma yanzu yana warkewa a asibiti.
A watan Mayu ma, an kai wa wasu masu yawon bude ido hari a Taj Mahal.
Wani mai rajin kare muhalli ya shaida wa Reuters cewa "Akwai birrai a ko ina a Agra."
Monkeys on a street Birrai a kan titiHakkin mallakar hotoYOGESH KUMAR SINGH
Image captionMazauna garin sun ce za a iya ganin birrai a kusan kowane titi a Agra
"Suna zuwa ne domin neman abinci, amma sai su yi kwace da kuma kai hari," in ji shi.
Mista Singh ya ce birrai suna kara fusata saboda sakamakon rashin wurin zamansu, wanda aka lalata ta hanyar fadada birnin.
Ya kuma kara da cewa wasu kungiyoyi na gida na kira da a samarwa birran maganin kashe cuta da kuma cire su daga tsarin kare karen namun daji.