[post by samaila umar lameedo]
An kama maza karuwai masu damfara a Kano

LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar `yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta cafke wasu mutum biyu da take zargin 'yan luwadi ne, wadanda ke amfani da kafofin sada zumunta suna tallata kansu.
Binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa mutanen su kan fara ne da kulla zumunci da mutane, amma daga baya sai su nemi a yi lalata da su, har su kan yi barazanar bata wa mutum suna idan bai ba su hadin kai ba.
Malamin Islamiyya ya yi wa yarinya 'fyade' a Kano
Masarautar Kano tana nan fiye da shekara 2000
Yadda ake 'binne layu' a wata makabarta a Kano
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano Sufurtanda Majiya ya ce matasan sun yi ta bibiyar wani attajiri har suka kulla alaka da shi, sannan suka fara yi masa barazana.
"Daga farko sun fara kiranshi ne suna yi masa godiya a matsayin makwabci ne ko mai hali da yake taimakawa... Daga karshe kuma sai suka bi shi da cewar ya ba su kudi. Ya ce kudin me? Sai suka ce kudin da ya yi amfani da shi," in ji Majiya.
'Yan sandan sun ce mutanen sun yi wa mutumin barazana cewa idan bai ba su kudi ba to za su bata masa suna a shafukan sada zumunta, cewa ya yi lalata da su.
Majiya ya kuma shaida wa wakilin BBC Ibrahim Isa cewa daga haka ne aka tsaurara bincike aka kuma kama su.
"Daya daga cikinsu ma ya tabbatar mana da cewa tun yana yaro wani dan uwansa ya fara lalata shi har shi kuma ya wuce da haka," in ji Sufurtanda Majiya.
Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar:
Luwadi ko madigo haramtaccen abu ne a tsarin dokokin Najeriya.