[post by samaila umar lameedo]
An gano yadda ganyen da ake saka alale ke maganin cututtuka

LABARAI DAGA 24BLOG
- Masu bincike a Najeriya sun gano yanda ganyen alala ke kare mutane da tsanantar cutukan koda da hanta
- Ganyen na dauke da sinadari mai yaki da cutar daji
- Sinadarin da ake samu a jikin kwayar shi yafi Vitamin C karfi
An gano yadda ganyen da ake saka alale ke maganin cututtuka
Ma'abota bincike a Najeriya sun gano cewa ganyen alala wanda aka sani da 'Thaumatococcus danielli' a kimiyyance yana kare tsanantar cutar ciwon suga da kuma hanta.
A takaice dai masu binciken sun gano cewa kwayar shi tana dauke da sinadarin da ke iya kare Dan adam daga cutar daji.
Binciken ya gano cewa sinadarin yafi sinadarin vitamin C karfi kuma za'a iya amfani dashi gurin fatattakar cutukan hanta da koda.
Anyi binciken ne akan beraye wanda ya nuna karfin ganyen Thaumatococcus danielli wajen fatattakar cutar koda da hanta.
Ganyen dai yana rukunin ganyayyakin Marantaceae. Ana kiranshi da ganyen al'ajabi. Yarbawa na kiran shi da 'Ewe-Eran ko Adundunmitan, inyamurai na kiranshi shi da' Akwukwo Elele.
Ana samun ganyen ne a Nahiyar Afirka