Zainab Ahmed: Me gwamnatin Najeriya ta ce kan kayyade iyali?

LABARAI DAGA 24BLOG
'Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan kalaman da wasu kafofin watsa labaran kasar suka ruwaito cewa, Minsitar Kudi Zainab Ahmed ta yi game da batun kayyade iyali.
A ranar Laraba ne jaridar Punch ta ruwaito cewa ministar ta ce "gwamnatin Najeriya na shirin kayyade yawan yaran da kowace mace za ta haifa a kasar."
Jaridar ta ce Zainab Ahmed ta fadi hakan ne a yayin wani taro da ke mayar da hankali kan tattalin arzikin Najeriya, a Abuja, babban birnin kasar.
Zainab Ahmed ta ce: "Kuma muna fatan da goyon bayan sarakunan gargajiya da malaman addinai, za mu kai gabar da za mu iya samar da wani tsari da zai kayyade wa mata yawan yaran da za su iya haifa, saboda hakan yana da muhimmanci wajen dorewar ci gabanmu.
Sai dai sa'o'i kadan bayan bayyanar labarin ne, Ministar ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter da ke cewa "Ba mu taba cewa za mu sa dokar kayyade iyali ba."
Sakon na ministar ya kara da cewa: "Gwamnatin tarayya tana ta ganawa da masu ruwa da tsaki kamar sarakunan gargajiya da malaman addinai don su bai wa mabiyansu shawara a kan ba da tazarar haihuwa.
"Ba mu taba cewa za mu sa doka kan kayyade iyali ba."
"Mene ne ba da tazarar haihuwa?
"Wannan wani abu ne da ke da muhimmanci wajen lafiyar mata, a dinga samun tazara tsakanin haihuwa."
A jawabin da rahotanni suka ambato ministar ta yi a wajen taron, ta ce daya daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta wajen cimma burin bunkasa tattalin arziki shi ne yawan al'ummar kasar.
"Muna ta ganawa da sarakunan gargajiya da sauran shugabanni. Mun gano cewa idan har muna so mu magance kalubalen da muke fuskanta wajen habaka tattalin arziki, wanda shi ne yawan al'umma, to lallai sai mun hada da sarakunan gargajiya," in ji ta.
Me 'yan Najeriya ke cewa?
Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya.
Wasu da dama sun ce idan ma har minsitar ta fadi hakan, to abu ne mai kyau wanda zai kawo wa kasar ci gaba, ganin irin dimbin al'ummar da take da su ba tare kuma da samun isassun abubuwan bukatar rayuwa ba.
Yayin da wasu kuma ke ganin hakan ba hurumin gwamnati ba ne.
Sai dai wasu kuma sun yi ta sukar kafafen watsa labaran da suke ganin sun "jirkita" labarin ne tun farko, ta hanyar sauya kalaman ministar.
Yawan al'ummar Najeriya
Najeriya dai ita ce kasar Afirkar da ta fi yawan al'umma, inda take da mutum miliyan 186.
Bincike ya nuna cewa yawan jama'a a Najeriya na karuwa akai-akai, wanda a kidiyar da aka yi a shekarar 1990 ya nuna kasar na da yawan jama'a miliyan 100, ya kuma karu da kashi 63 cikin 100 a kan wadda aka yi a shekarar 2006, inda yawan al'ummar ya kai miliyan 140.
Ko a watan Afrilun shekarar 2018 ma
Hukumar Kidiya ta kasar NPC ta ce yawan al'ummar Najeriya ya kusa kai wa miliyan 200 .
A cewar Ma jalisar Dinkin Duniya kuwa, Najeriya na dab da zama kasa ta uku mafi yawan al'umma a duniya bayan China da Indiya, nan da tsakiyar karnin da muke ciki.
Ta yi gargadi kan irin kalubalen da hakan zai kawo ta wajen samar da ilimi da inganta harkar kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.
A yanzu haka dai kasar ce ta bakwai a yawan al'umma a duniya.
Duk da irin arzikin da Allah ya yi wa Najeriya, akasarin jama'arta na rayuwa kan kasa da dala daya a rana, yayin da da yawansu ke zaune a karkara.
Wannan ya sa a kowace shekara ana samun mutanan da ke kaura daga kauyuka zuwa manyan birane domin samun saukin rayuwa.
Me shugabannin al'umma ke yi?
Malamai da sarakunan al'umma daban-daban sun sha yin tsokaci kan yadda ake haifar yara barkatai ba tare da tanadar musu abin da suke bukata don samun ingantacciyar rayuwa ba.
A watan Fabrairun 2007 ne aka ruwaio
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II yana cewa majalisarsa tana shirye-shiryen gabatar da wata doka da za ta hana mazan da ba su da karfi auren mata fiye da daya a jihar .
Sarkin ya yi nuni da cewa abin takaici ne yadda za a ga mutum "yana fama da cin yau da na gobe, amma zai auri mace fiye da daya.
"Ya kuma haifi 'ya'ya masu yawan da ba zai iya ciyar da su, ko tufatar da su, ko samar musu da isasshen muhalli ba, ballantana ya ba su irin tarbiyyar da al'umma za ta yi alfahari da su."
Sai dai a wancan lokaci kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce.
A watan Afrilun 2018 ma a wata hira da BBC ta yi da shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, an tambaye shi matsayin tsarin iyali a Musulunci.
Malamin ya masa da cewa: "Idan ka san za ka haifi mutum ba za ka ba shi ilimi ba, ba za ka yi masa tarbiya ba, ba za ka kula da shi ba, to ka ga gara ka haifi kadan, da ka haifi masu yawan da ba su da amfani."