Zaben 2019: An hana Buhari da Atiku kashe fiye da ₦5 biliyan

LABARAI DAGA 24BLOG
Majalisar Dokokin Najeriya ta kafa wata doka da ta kayyade kudaden da 'yan takara za su iya kashewa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2019.
Dokar ta hana 'yan takara kashe kudaden zabe da suka zarce wadannan:
'Yan takarar mukamin shugaban kasa: Kada ya wuce naira biliyan biyar
'Yan takarar mukamin gwamna: Kada ya wuce naira biliyan daya
'Yan takarar mukamin majalisar dattawa: Kada ya wuce naira miliyan 250
'Yan takarar mukamin majalisar wakilai: Kada ya wuce naira miliyan 100
Zaben 2019: Dole a yi amfani da na'urar 'Card Reader'
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudin zaben 2019
Dokar zaben kuma ta bayyana yadda za a yi amfani da na'urar zabe ta 'Card Reader' a lokacin tantance masu kada kuri'a a rumfunan zabe.
Wakilin BBC, Aliyu Tanko daga birnin Legas ya ce wannan matakin na neman rage yadda ake amfani da kudi a wajen gudanar da zabukan da suka gabata a kasar.
An yi amfani da na'urorin tantance masu kada kuri'a a zaben na 2015, amma an rika samun korafe-korafe cewa ba sa aiki a wasu lokutan, musamman ma a yankunan da ake fama da rashin hasken lantarki.
A karkashi wannan dokar, ya zama wajibi a yi amfani da na'urar tantance masu kada kuri'ar, amma idan aka samu tangarda kuma ba a iya maye gurbinta da wata ba cikin sa'a uku, to za soke zaben da aka gudanar a wannan akwatin, kana a sake gudanar da wani sabon zaben cikin sa'o'i 24.