Zaben 2019: Dole a yi amfani da na'urar 'Card Reader'

LABARAI DAGA 24BLOG
Majalisar dattawan Najeriya ta sake dubawa tare da amincewa da gyaran fuska ga dokar zaben kasar.
Shugaban kwamitin nazari kan dokar zaben, Sanata Nazif Gamawa ya shaidawa BBC cewa sun yi wa dokar gyaran da zai sa ta samu karbuwa ga bangaren zartarwa.
An dai sha takaddama tsakanin bangaren majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa game da dokar.
Amma ya ce duk abin da shugaban kasa bai amince da shi ba sun cire a dokar zaben. Kuma suna kyautata zaton shugaban zai amince da dokar.
Batun amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a na daga cikin gyaran da 'yan majalisar suka yi.
Sanata Nazif ya ce sun amince cewa dole sai da Card reader za a yi zaben. "Idan babu card reader babu zabe gaba daya," in ji shi.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudin zaben 2019
Obasanjo ya goyi bayan Atiku a zaben 2019
Yadda Paul Biya ya sake lashe zaben shugaban Kamaru
Sanatan ya ce duk abin da shugaban kasa bai amince da shi ba sun cire a dokar zaben. Kuma suna kyautata zaton shugaban zai amince da dokar.
Ya ce idan a ranar zabe aka kawo na'urar da ba ta aiki ko kuma ana cikin zabe ta daina aiki, kuma ba a canza ba zuwa awa uku kafin a rufe zabe to dole a dage zaben zuwa washegari domin a yi tanadin sabuwar na'ura Card Reader.
Majalisar ta ce dokar zaben ta yi tanadin cewa dole a tabbatar da hukumar zabe tana da isassun card reader a ranakun zabe.
Karo uku Majalisar na turawa shugaban kasa domin ya sanya hannu amma yana dawo wa da dokar.
Rashin amincewa da dokar ya janyo suka daga bangaren 'yan adawa inda suke zargin cewa shugaban ya ki sanya hannu kan dokar ne saboda ba ya son a yi amfani da na'urar, zargin da fadar shugaban kasa ta musunta.