Online counter

Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

LABARAI DAGA 24BLOG
Bukola Saraki, shuaban majalisar dattawa da Yakbu Dogara, kakakin majalisar wakilai basu halarci Eagle Square Abuja ba inda ake bikin shekaru 58 da samun yancin kan Najeriya wanda manyan masu fada aji da jiga-jigan kasar suka halarta.
Wadanda suka halarci faretin sun hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da maaimakinsa, Yemi Osinbajo, Walter Onnoghen, alkalin alkalan Najeriya, da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon, da sauran manyan masu fada aji.
Sojin kasar za su yifareti don girmamawa sannan a fito da hotuna dake nuni ga tarihin Najeriya da kuma liyaar ranar yancin kai.
Duk kokari da akayi domin Magana gaYusuph Olaniyonu, kakakin Saraki bai samu ba, kakakin Dogara kuma, Turaki Hassan yace baida masaniyar ko an gayyaci ubanidansa ko kuma dalilin day a hana shi zuwa.

Post a Comment

0 Comments