Yanzu-Yanzu: Kakakin majalisa a wata jihar Arewa ya sauya sheka zuwa APC daga PDP

LABARAI DAGA 24BLOG
- Tsohon kakakin majalisar jihar Benue ya sauya sheka zuwa APC daga PDP
- Yace Gwamnan jihar baya kokari
Tsohon kakakin majalisar jihar Benue Mista Stephen Tsav ya sanar da ficewar sa daga jam'iyya mai mulki a jihar ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressive Congress (APC) da daren ranar Juma'a.
Yanzu-Yanzu: Kakakin majalisa a wata jihar Arewa ya sauya sheka zuwa APC daga PDP
Mista Tsav dai ya bayyana ficewar ta sa ne a mahaifar sa ta Guma inda ya bayyana cewa ya yanke shawarar fitar ne duk kuwa da irin tsabar kudaden da ya ansa da nufin hanashi sauya shekar.
Samu cewa shima dai daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ta APC a jihar Sanata George Akume da yake jawabi a wurin karbar sa ya caccaki salon mulkin gwamnan jihar da ya bayyana da wanda ya gaza a dukkan fannoni.