'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya

LABARAI DAGA 24BLOG
Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Abia dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya a ranar litinin din da ta bata ta sanar da soma wani kwakkwaran bincike akan kisan gillar da aka yi wa wasu manyan malaman addinin kirista a garin Umuobia a watannin baya.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar, SP Geoffrey Ogbonna shine ya sanar wa da majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai hakan a garin Umuahia, babban birnin jihar ta Abia.
'Yan sandan Najeriya sun soma binciken kisan manyan malaman addini a Najeriya
samu cewa manyan malaman da aka kashe sun hada da Fasto Kelechi Iwuanyanwu da ke shugabantar majami'ar Winds of Glory, da kuma Fasto Ogbonna.
A wani labarin kuma, Wani rahoto da muka samu daga majiyar mu ta ThisDay yana nuni ne da cewa masu fada aji na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Legas sun dage kan lallai lallai sai an tsige gwamnan jihar Akinwunmi Ambode kafin zaben 2019.
Haka ma dai rahoton ya bankado cewa tuni ma har shire-shire sun kammala na tabbatar da tsige gwamnan da zarar kurar zabukan fitar da gwanin nan ta dan lafa.