'Yan majalisar tarayya 62 na shire-shiren ficewa daga jam'iyyar APC

LABARAI DAGA 24BLOG
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu daban daban yanzu haka na nuni ne da cewa akalla 'yan majalisun da suka kai 62 ne ke ta kulle-kulle na ficewa daga jam'iyyar APC idan dai har ba'a basu tikitin takara a jam'iyyar ba na zaben 2019.
Binciken da muka gudanar dai ya tabbatar mana da cewa akalla 'yan majalisar 70 ne daga jam'iyyar ta APC ke basu samu tikitin takara ba a zaben 2019 wanda kuma suka rubuta takardar koke suna kalubalantar hakan.
Rigimar duniya: 'Yan majalisar tarayya 62 na shire-shiren ficewa daga jam'iyyar APC
Samu cewa bayan haka nan kuma 'yan majalisun a baya sun gana da shugaba Buhari wanda ya basu hakuri tare da tabbatar masu da cewa jam'iyyar ta APC zata yi masu adalci.
Sai dai kuma kwamitin da aka dorawa alhakin sauraron koken na 'yan takarar bayan zaman da ya gudanar daga baya ya yi fatali da dukkan koken na su sai na mutane 8 kacal.
Yanzu dai tuni jam'iyyar ta APC ta mika sunayen 'yan takarar da take so su tsaya mata inda tuni kuma ta tabbata cewa ba bu sunayen 'yan majalisun a cikin su.