'Yan bindiga sun sace wasu malaman addini 5 a Najeriya

LABARAI DAGA 24BLOG
Wasu da ake tunanin masu satar mutane ne dauke da muggan makamai sun sace wasu malaman addinin kirista biyar mata a karamar hukumar Issele-Uku, dake a jihar Delta dake a yankin kudu maso kudancin Najeriya.
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, an dai sace matan ne suna kan hanyar su ta dawowa daga wurin bizne wani dan majami'ar su a kusa da hanyar jirgin kasan dake a unguwar Ika.
'Yan bindiga sun sace wasu malaman addini 5 a Najeriya
Legit.ng Hausa ta samu cewa 'yan bindigar sun tare motar da malaman addinin ke ciki ne sannan kuma suka yi ta harbe-harbe a sama wanda yayi sanadiyyar jikkata biyu daga cikin mutanen dake a motar kafin daga bisani su arce da biyar daga cikin su.
Kwamishinan 'yan sadan Najeriya a jihar dai Muhammad Mustafa ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan kuma ya bayar da tabbacin jami'an sa za su kubutar da su cikin kankanin lokaci.