'Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Zamfara

LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar 'yan sanda jihar Zamfara ta ce akalla mutum shida sun rasa rayukansu ciki harda jami'in dan sanda guda a wani harin bindiga da aka kai kauyen Gurbin Baure da ke karamar hukumar Zurmi.
Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar SP Muhammad Shehu, ya shaida wa BBC cewa 'yan bindiga ne da babu adadi suka farwa kauyen a cikin daren Juma'a, inda suka yi ta harbi da kone-kone.
Sai dai a cewar jami'in duk da cewa da farko sun yi kokarin cin karfinsu daga bisani an murkushe su da taimakon jami'an soji.
An sace 'yan mata tagwaye da aka kusa bikinsu a Zamfara
An kashe mutum 20 suna sallah a Zamfara
'An kashe mutum 31 a Zamfara'
Mataimakin shugaban karamar hukumar ta zurmi Abubakar Muhammad ya shaidawa BBC cewa mutane na cikin zulumi.
Ya kuma ce gawarwaki takwas suka kidaya da na jami'in dan sanda guda ba shida kamar yadda rundunar 'yan sanda ke cewa ba.
Kusan shekara guda kenan da ake fuskantar irin wadanan hare-hare a Zurmi duk da matakan da hukumomi da girke jami'an tsaro a yankin da aka ce an yi