Yadda gwamnatin Najeriya ke raba wa 'talakawa' N5,000

LABARAI DAGA 24BLOG
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken rahoton:
Najeriya, kamar wasu kasashen Afirka ta fara aiwatar da shirin tallafa wa gajiyayyu da sauran mutane masu rauni da naira dubu biyar kowane wata da nufin rage musu radadin talauci.
Yayin da wasu ke yabawa da yadda shirin ke inganta rayuwar marasa galihu, wasu kuma na sukar yadda ake aiwatar da shi, suna zargin cewa ana nuna bambancin siyasa.
Ibrahim Isa ya yi nazarin shirin, ga kuma rahoton da ya hada mana.