Wasu tsinannun barayi sun sace takalman Annabi Muhammadu SAW a Fakistan

LABARAI DAGA 24BLOG
- Wasu tsinannun barayi sun sace takalman Annabi Muhammadu SAW
- A kasar Fakistan ne suka sace takalman
- An dai kafa kwamitin da zai yi bincike kan hakan
Kimanin shekaru 16 da suka gabata, an samu aukuwar wata irin sata mai ban takaici da ban mamaki a kasar Fakistan inda wasu suka sace takalman da ake kyautata zaton su ne fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu SAW yayi anfani da su a lokacin rayuwar sa.
Wasu tsinannun barayi sun sace takalman Annabi Muhammadu SAW a Fakistan
Kamar dai yadda muka samu, barayin dai sun sace takalman ne a ranar 30 ga watan Yuli, 2002 a inda suke aje masallacin Badshahi a can kasar ta Fakistan.
Legit.ng Hausa dai sun samu cewa takalman na manzon Allah sun kasance a kasar ta Fakistan da dadewa kuma al'ummomi daga kasashe daban daban kan zo domin ganin takalman .
Yanzu dai haka wani alkali a kasar ya sa an kafa kwamitin bincike na musamman da nufin binciko barayin da ya ce sun tafka abun kunyar da ba'a taba yi ba a tarihin duniya.
Haka ma dai tuni har an saka gagarumar kyauta ta Dalar Amurka dubu 15 ga dukkan wanda ya bayar da cikakken bayanai game da yadda za'a gano barayin