Wasu mata 'yan APC sun sha alwashin zuwa Abuja tsirara saboda dan takarar gwamna

LABARAI DAGA 24BLOG
Wasu kungiyoyin mata masu goyon bayan jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a jihar Ogun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun sha alwashin yin zanga-zanga a tsirara har Abuja don nuna goyon bayan su ga wani dan takarar gwamna.
Shi dai dan takarar gwamnan da wadannan matan ke goyon bayan sunan sa Adekunle Akinlade kuma kuma shine wanda gwamnan jihar mai ci yanzu Ibikunle Amosun yake so amma kuma bai ci zaben fitar da gwani ba da aka gudanar.
Wasu mata 'yan APC sun sha alwashin zuwa Abuja tsirara saboda dan takarar gwamna
A ranar Laraba, matan sun yi ta jerin gwano a manyan titunan garin Abeokuta suna zanga-zanga tare da furta kalaman kin jini ga shugaban jam'iyyar ta APC, Kwamared Adams Oshiomhole.
Zabukan fitar da gwanin na jam'iyyar APC dai ya bar baya da kura a jahohi da dama na kasar nan inda da yawa suke ganin tamkar ba'a yi masu adalci ba.