Tsohon shugaban CIA ya dora laifin sakon bama-bamai a kan Trump

LABARAI DAGA 24BLOG
Tsohon babban jami'in hukumar liken asirin Amurka, CIA, John Brennan daya daga cikin wadanda aka aika wa kunshin na bam ya dora laifin a kan Trump musamnan kan irin kalamansa na nuna kiyayya.
Mista Brennan ya ce dole ne Trump ya sake tunani kan irin furucinsa da kuma abin da yake yi, ya ce ya kamata a ce hada kan 'yan kasa ne ya sa gaba, maimakon rarraba kai.
Jawabin Obama yana sa dadin bacci - Trump
An zargi Trump da bai wa 'karuwai' toshiyar baki
Donald Trump ya bayyana bama-baman da aka aika wa manyan 'yan jam'iyyar Democrat ciki har da tsohon shugaban kasar Barack Obama da tsohuwar Sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton, a matsayin hari ga dumokuradiyya.
A yayin da yake jawabi wajen wani gangamin siyasa a Winsconsin, Shugaba Trump ya ce bai kamata Amurkawa su bari wani bambanci ya raba su ba.
Kuma ya lashi takobin cewa za a gano wadanda ke da hannu a lamarin sannan su fuskanci hukunci.
Ya kara da cewa babban aikinsa, kamar yadda aka sani a matsayin shugaba, shi ne ya tabbatar da zaman lafiyar Amurka. ''Wannan shi ne abin da muke magana a kai. Kuma shi muke yi.'' In ji shi.
Mista Trump ya ce dole ne wadanda ke cikin fagen siyasa su daina daukar abokan hamayya abin kyamata.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurkar FBI ta tabbatar da cewa akwai karin wasu sakwanni na bama-baman guda biyu da aka tura wa wasu 'yan majalisa na jam'iyyar ta Democrat, manyan masu hamayya da gwamnatin Trump.
Yanzu jimillar guda takwas ke nan hukumar ke bincike a kai da aka yi kokarin tarewa Kafin isa ga manyan 'yan siyasar na Amurka.
An dai gano bama-baman ne a yayin gudanar da binciken sakonnin. Kuma Babu ko da daya daga cikin kunshin abubuwan da ya fashe kuma babu wanda ya ji rauni.
Zuwa yanzu babu wani ko wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin tura sakwannin da kuma manufar aikawa da su.