Online counter

Tsohon jigon APC ya yaba da sabon mukamin da Atiku ya ba Saraki

Tsohon jigon APC ya yaba da sabon mukamin da Atiku ya ba Saraki

LABARAI DAGA 24BLOG
A wata sanarwa a ranar Talata, 16 ga watan Oktoba Frank yace da wannan tawaga da PDP ta hada, babu shakka za su kayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC.
Ya ci gaba da cewa saboda shahara da soyayyar da ├Żan Najeriya ke yiwa mafi akasarin mutanen da PDP ta hada a tawagar kamfen din, toh babu shakka jam’iyyar adawa zata zamo mai nasara a zaben 2019.
Sauran mutanen da aka ba mukamen sun hada da Gwamna Aminu Tambuwal (Sokoto, arewa ta yamma), Ibrahim Dankwambo (Gombe, arewa ta gabas), Samuel Ortom (Benue, arewa ta tsakiya), Nyesom Wike (Rivers, kudu maso kudu), Dave Umahi (Ebonyi, kudu maso gabas), yayinda tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayo Fayose, zai kula da kudu maso yamma.

Post a Comment

0 Comments