Tirkashi: Labarin wata mata da ta haifi 'ya'ya 44 duk ita kadai a rayuwar ta

LABARAI DAGA 24BLOG
- Labarin wata mata da ta haifi 'ya'ya 44 duk ita kadai a rayuwar ta
- Sunan ta Mariam Nabatazi kuma 'yar kasar Uganda ce
A wannan zamanin da magidanta kan haifi 'ya'ya biyu zuwa hudu kacal sakamakon sauye-sauyen rayuwa, an samu wata mata da ta ciri kambun macen da ta fi kowace mace haihuwa a 'yan shekarun nan mai suna Mariam Nabatazi.
Tirkashi: Labarin wata mata da ta haifi 'ya'ya 44 duk ita kadai a rayuwar ta
Ita dai kamar yadda muka samu, Mariam Nabatazi Allah ya albarkace ta da haihuwar 'ya'ya 44 a tsawon shekarun ta 40 kacal a duniya wanda hakan ba kasafai akan samu hakan ba.
Legit.ng Hausa ta samu cewa rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa Mariam Nabatazi dake zaman 'yar asalin kasar Uganda ta haifi 'yan biyu sau shidda, 'yan uku sau hudu sai kuma 'yan hudu sau uku a rayuwar ta.
Haka zalika ta haifi wasu 'ya'yan su kadai har sau biyu sai dai kuma wasu daga cikin 'ya'yan nata basu rayuba domin sun rasu tun suna 'yan jarirai.