Sai an yiwa PDP dagaske a zaben 2019 - Gwamna Bello

LABARAI DAGA 24BLOG
Mun samu cewa a daren ranar Larabar da ta gabata ne Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa dole ne sai jam'iyyar APC ta mike tsaye tukuru domin jajircewa akan jam'iyyar adawa ta PDP a yayin babban zabe na 2019.
Gwamna Bello ya bayyana cewa matukar jam'iyyar APC na hankoron samun nasara a babban zabe na badi to kuwa sai ta zage dantsenta da gaske akan jam'iyyar PDP domin cimma wannan kudiri.
Gwamnan ya yi wannan gargadi gami da jan kunne yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama matasan 'yan majalisarsa da wata liyafar dare a fadarsa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.
Sai an yiwa PDP dagaske a zaben 2019 - Gwamna Bello
A cewarsa, dole ne jam'iyyar APC ta fito kwanta da kwarkwata tare da baja kolin kwazon shugaba Buhari na shekaru ukun da suka gabata domin tabbatar da nasararsa a zaben 2019.
Ya ci gab cewa, kada jam'iyyar APC ta yi kuskuren bai wa jam'iyyar adawa dama ta karbar ragamar mulkin kasar nan a zaben 2019, inda ya jaddada cewa shugaba Buhari shine mafi cancantar jagorancin kasar nan da zai fidda ita zuwa ga Tudun tsira.
A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren aiki na tashar filin jirgin sama dake birnin Fatakwal na jihar Ribas.