Sahle-Work Zewde: Mace ta farko da za ta shugabanci Habasha

LABARAI DAGA 24BLOG
'Yan majalisar dokokin kasar Habasha sun zabi Sahle-Work Zewde a matsayin mace ta farko da za ta jagoranci kasar.
Misis Sahle-Work kwararriyar ma'aikaciyar diflomasiyya ce wadda a baya-bayan nan ta yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya.
An zabe ta wannan mukamin na jeka na yi ka ne mako guda bayan da firai minista Abiy Ahmed ya nada sabbin ministocin gwamnatinsa, inda rabin ministocin mata ne.
A jawabin da ta yi bayan an nada ta. Shugaba Sahle-Work ta jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin al'ummar kasar.
Habasha da Eritrea sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Jirgin saman Habasha ya yi tafiyar tarihi zuwa Eritrea
Mata nawa ne suka shugabanci kasashe a Afirka?
Kasar Mauritius ce kasar Afirka da ta taba samun mata uku da suka taba shugabantarta a lokuta daban-daban.
Amma a fadin nahiyar Afirka, kawo yanzu an samu mata takwas da suka rike mukamin shugaban kasa.
Wadansunsu an nada su ne, su yi rikon mukamin kafin a gudanar da zabe (kamar yadda ya kasance a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Afirka ta Kudu).
Wasu kuma sun dare mukamin ne bayan mutuwar shugaban kasa mai ci (kamar yadda ya faru a kasashen Malawi da Gabon).
Ga cikakken jadawalin matan da suka taba zama shugabannin kasashe a Afirka:
1. Sylvie Kinigi
An haifi Sylvie Kinigi a 1953, kuma ita ce mace da ta rike mukamin mukaddashiyar shugabar kasa a Burundi daga 1993 zuwa 1994.
Ta rike mukamin firai ministar kasar Burundi daga 10 ga watan Yulin 1993 har zuwa 7 ga Fabrairun 1994.
Daga baya ne aka nada ta ga mukamin mukaddashin shugabar kasa inda ta kasance mace ta farko da ta rike wadannan mukaman a fadin kasar ta Burundi.
2. Agnès Monique Ohsan Bellepeau
An haifi Agnes Bellepeau a 1942, kuma 'yar siyasa ce a kasar Mauritius, inda ta taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 2010 zuwa 2016.
Ta taba rike mukamin mukaddashin shugabar kasar daga 31 ga watan Maris zuwa 21 ga watan Yulin 2012 a lokacin da tsohon shugaban kasar Sir Anerood Jugnauth ya ajiye aiki har zuwa lokacin da aka rantsar da Kailash Purryag a matsayin sabon shugaban kasa.
Ta sake rike mukamin mukaddashin shugaban kasa daga 29 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Yuni na 2015 a lokacin da shi ma Kailash Purryag ya yi murabus, har zuwa lokacin da aka rantsar da wata macen - Ameenah Gurib-Fakim.
3. Ameenah Gurib-Fakim
An haifi Amina Gurib born 17 ga watan Oktoba 1959, kuma kwararriya ce a fagen kimiyya.
Ta zama shugabar kasar Mauritius ta shida daga 2015 zuwa 2018.
An tsayar da ita 'yar takarar mukamin shugaban kasa a jam'iyyar Alliance Lepep a watan Disambar 2014.
Misis Gurib-Fakim ce mace ta farko da aka zaba kai tsaye a matsayin shugabar kasar, kuma ita ce mace ta uku da ta rike mukamin shugaban kasa bayan Sarauniya Elizabeth ta biyu da Monique Ohsan Bellepeau.
4. Ellen Sirleaf
Ellen Johnson Sirleaf ta shugabanci kasar Laberiya na tsawon shekara 12 tun da aka zabe ta ga mukamin a shekarar 2006.
Ita ce kuma mace ta farko da aka taba zaba kai tsaye ga mukamin shugaban wata kasa a fadin nahiyar Afirka.
An haife ta ne a a birnin Monrovia a ranar 29 ga watan Oktobar 1938, kuma ita ce shugabar Laberiya ta 24.
Ya yi mulkin ne tsakanin shekarar 2006 zuwa 2018.
Mahaifinta dan kabilar Gola ne amma mahaifiyarta ruwa biyu ce - rabinta 'yar kabilar Kru ce, rabi kuma Bajamushiya ce.
5. Ivy Matsepe-Casaburri
An haifi Ivy Matsepe a ranar 18 ga watan Satumba 1937, kuma 'yar siyasa ce daga kasar Afirka ta Kudu.
Ta rike mukamin shugabar Afirka ta Kudu na tsawon sa'a 14 ne kacal a watan Satumbar 2008 bayan da tsohon shugaban kasar Thabo Mbeki ya ajiye aiki, kafin aka nada Kgalema Motlanthe a matsayin sabon shugaban kasa.
Ta kuma rike mukamin mukaddashin shugaban kasar a shekarar 2005, yayin da shugaba Thabo Mbeki da mataimakinsa suka kasance ba sa cikin kasar.
6. Catherine Samba-Panza
An haifi Catherine Samba-Panza a ranar 26 ga watan Yunin 1956, kuma ta rike mukamin shugaban kasa ta riko a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka daga 2014 zuwa 2016.
Ita ce mace ta farko da ta fara zama shugaban kasa a duk tarihin kasar.
Kafin ta dare wannan mukamin, ta taba rike mukamin magajin garin Bangui daga 2013 zuwa 2014.
7. Rose Francine Rogombé
An haifi Rose Farncine Rogombé a ranar 20 ga watan Satumbar 1942, kuma ta rasu a ranar 10 ga watan Afrilu 2015.
Rose Francine 'yar siyasa ce wadda ta taba rike mukamin mukaddashin shugabar kasar Gabon daga watan Yunin 2009 zuwa Oktobar 2009, bayan mutuwar tsohon Shugaba Omar Bongo.
Ta gaji marigayin ne saboda mukaminta na shugabar majalisar dattawar kasar, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
Misis Rose lauya ce, kuma mamba ce ta jam'iyyar siyasa ta Gabonese Democratic Party (PDG).
Ita ce mace ta farko da ta taba rike wannan mukami na shugaban kasa, amma ta koma ga mukaminta na shugabar majalisar dattawa bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasa.