Rikicin Kaduna: Me El-Rufai ya tattauna da shugabannin addini?

LABARAI DAGA 24BLOG
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya yi wani taro da wasu shugabannin al'umma da kuma sarakunan gargajiya na yankuna biyar na kwaryar garin Kaduna, musamman shugabannin yankunan da ake samun tashe tashen hankula.
Mai magana da yawun gwamnan, Samuel Aruwan ya ce makasudin taron, wanda aka yi shi a ranar Alhamis shi ne domin gwamnatin jiha ta sanar da shugabannin kungiyoyin Musulmai da na Kirista, da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki muhimmancin sanya hannunsu don kawo karshen irin rikicin da ke faruwa a jihar.
Ya kara da cewa duk da cewa irin wannan taron ba sabon abu ba ne, wannan din ya zo ne a gaggauce don a magance rikicin kabilancin da ke faruwa a jihar.
Hanyoyi hudu da za a bi a magance rikicin Kaduna
Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Kaduna ya shafa
Mutum 55 aka kashe a rikicin Kaduna - 'Yan sanda
Ga dai hirar da wakilin BBC Nurah Ringim ya yi da Samuel Aruwan.
Sai a latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraro:
A ranar Juma'a ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 wato ba dare ba rana a garin Kaduna da Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru bayan barkewar rikici.
Kimanin mutum 55 ne 'yan sanda suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rikicin.
A baya dai an sha samun rikice-rikicen kabilanci da addini a garin Kasuwar Magani.
A wannan karon ma, rahotanni na cewa rikicin ba ya rasa nasaba da kabilanci da addini.