LABARAI DAGA 24BLOG
A yayin da ya ke shirin barin jihar Kano Mawallafin Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar ya bayyanawa manema Labarai cewa, "matukar suka ci gaba da karyata ni suna cewa kazafi nake yi musu zan ci gaba da sako ragowar Bidiyon. Da farko na sako daya na sako na biyu to zan ci gaba da sako ragowar."
Da aka tambaye shi dangane da sha'anin tsaro ya yabawa rundunar 'yansandan jihar Kano na yadda suka ba shi tsaro. "Ni ba dan kowa ba amma mataimakin Kwamishinan 'yansanda uku ne suka tare ni baya ga Jami'an tsaro ko ina rike da Bindigogi".