Online counter

Manyan ‘Yan siyasan da ake hangen za su iya zama Mataimakin Atiku Abubakar a PDP

Manyan ‘Yan siyasan da ake hangen za su iya zama Mataimakin Atiku Abubakar a PDP

LABARAI DAGA 24BLOG
1. Peter Obi
Wasu na ganin cewa Atiku zai nemi ya tsaida Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasan sa a 2019. Obi dai tsohon Gwamna ne na Jihar Anambra wanda ya san aiki ya kuma iya Magana game da farin jini.
2. Ben Murray Bruce
Sanata Ben Bruce yana cikin sahun wadanda ake tunani Atiku zai tafi da su a 2019. Sanatan na Bayelsa ta Gabas dai ba zai koma kujerar sa ba don haka ake ganin cewa watakila ya bi Atiku Abubakar wanda tun ba yau ba su ke tare a PDP.
3. Oby Ezekwesili
Tsohuwar Ministar ilmin kasar nan Oby Ezekwesili tana cikin mutanen da ake ganin Atiku na iya zama ta masa Mataimakiyar Shugabar kasa. Oby za ta samu karbuwa a wajen manyan ‘Yan Boko da kuma Mata musamman a Kudancin kasar nan.
4. Ngozi Okonjo Iweala
Wata matar da ake kishin-kishin din cewa Atiku zai zama yayi takara da ita a 2019 ita ce Okonjo Iweala wanda tayi Ministar kudi har sau 2 a Najeriya. Iweala dai ta san harkar tattali kuma ita ma tayi aiki da Atiku a lokacin Gwamnatin Obasanjo.
5. Akinwumi Adesina
Na karshe a jerin da ake ganin Atiku na iya zabowa a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a PDP shi ne Adesina wanda yanzu shi ne Shugaban bankin nan na cigaban Afrika. Adesina Bayarabe ne da ya rike Ministan noma a Gwamnatin PDP.

Post a comment

0 Comments