Manjo Al-Mustapha ya fadi manyan abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasa

LABARAI DAGA 24BLOG
- Manjo Al-Mustapha ya fadi manyan abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasa
- Yace zai mayar da Najeriya bisa turba madaidaiciya
- Ya caccaki salon mulkin shugaba Buhari
Tsohon dogari ga tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi alkawarin maido da kasar nan akan turba madaidaiciya idan dai har aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2019.
Zaben 2019: Manjo Al-Mustapha ya fadi manyan abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasa
Manjo Al-Mustapha da ke zaman dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PPN ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewar idan har ya zama shugaban kasa to tabbas zai yi kokari wajen ganin ya gyara tabarbarewar da harkokin sukayi a wannan mulkin na Shugaba Buhari.
Haka zalika ya bayyana cewa yan kasar sun cancanci kyakkyawan shugabanci a dukkan matakai shi yasa ma ya ga ya dace ya fito takarar domin ya cece su daga kangin mugun shugabancin da suke ciki.
A wani labarin kuma, Wani faifan bidiyo da yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani na wasu 'yan mata tsala-tsala suka ta fada a tsakanin su saboda saurayi ya na ta yawo a kafafen sadarwar zamani tamkar wutar jeji.
Kamar dai yadda wani namiji da ya dauki 'yan matan suna fadan kuma ya yada a dandalin sadarwar zamani, ya bayyana cewa abun takaicin da ya saka matan fada shine wani saurayin da da alama ya yaudare su su duka kuma ya tafi ya bar su.