Mai tattare da ce-ce-ku-ce ya zama Firaminista

LABARAI DAGA 24BLOG
An sanar da daya daga cikin fitattaun 'yan siyasar Sri Lanka da ake ce-ce-ku-ce a kan shi a matsayin sabon Firaministan kasar.
Mahinda Rajapaksa da ake zargi da alhakin mutuwar dubban fararen hula a lokacin yakin basasar kasar, ana danganta halin tattalin arzikin da kasar ta fada da tarin bashin da ke kanta a kan tsarinsa na tattalin arziki.
Sai dai kuma tsohon abokin hamayarsa Shugaba Maithripala Sirisena ya zabe shi domin ya maye gurbin Ranil Wickremesinghe.
Ko dayake tsohon firaministan ya dage a kan cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba, kuma zai kalubalanci korar da aka masa a kotu.
Mista Wickremesinghe ya ce har yanzu shi ke umarta mafi rinjaye a majalisar dokokin kasar, duk da cewa jam'iyyar shugaban kasar ta janye daga hadakar sa.
An dai jima ana fuskantar rashin jituwa tsakanin Mista Sirisena da Mista Wickremesinghe a kan tsare-tsaren tattalin arziki da kuma yanayin tafiyar da al'amuran gwamnati.