Online counter

Ku ceto Leah Sharibu yanzu ba tare da bata lokaci ba – Atiku ga gwamnatin tarayya

Ku ceto Leah Sharibu yanzu ba tare da bata lokaci ba – Atiku ga gwamnatin tarayya

LABARAI DAGA 24BLOG
Atiku a fadi hakan a shafinsa na twitter yayinda yake martani ga kisan wata ma’aikaciyar agaji, Hawa Liman da yan ta’addan suka yi.
Ya ce: “Ina matukar bakin ciki da kisan Hauwa Liman, ma’aikaciyar ICRC, da ýan Boko Haram suka yi.
“Ina fatan gwamnatin tarayya zata tura duk matakan day a kamata domin dawo da Leah Sharibu da dukkanin yaran dake tsare a hannun Boko Haram gidansu."
Wata ballin kungiyar Boko Haram mai suna Daular Musulunci da yankin Afrika maso yamma wato ISWAP ta kashe daya daga cikin ma’aikatan kungiyar agajin Red Cross, Hauwa Liman, bayan wa’adin da suka baiwa gwamnatin tarayya ya cika a yau.
Yan ta’addan sunyi alkawarin cewa ba zasu kashe Leah Sharibu ba amma ta zama baiwa har abada. Jaridar The Cable ta samu rahoto.

Post a Comment

0 Comments