Online counter

Kotu ta takawa APC birki a kan taba 'yan takarar jihar Zamfara

Kotu ta takawa APC birki a kan taba 'yan takarar jihar Zamfara

LABARAI DAGA 24BLOG
Babban kotun jihar Zamfara ta yanke wani hukuci na dakatar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) daga soke 'yan takarar zabe daga jihar a babban zaben 2019.
Justice Mukhtar Yushau ne ya bayar da wannan umurnin a yau Talata bayan wasu manyan mambobin jam'iyyar a Jihar sun shigar da kara a kotun.
A karar da suka shigar, jiga-jigan na jam'iyyar sun kalubalanci ikon da uwar jam'iyyar ta APC da INEC ke dashi na soke dukkan 'yan takarar zabe da ke jihar a zaben 2019 mai zuwa.
Sun shigar da karar ne a ranar 8 ga watan Oktoba a madadin sauran 'yan takara 24 da ke jihar ta hannun lauyansu, Mohammad Sani Katu.
Alkalin kotun ya umurc uwar jam'iyyar da shugaban jam'iyyar na yankin Arewa maso Yamma da kuma INEC su kame kansu daga daukan wata mataki na hana 'yan takarar ikon shiga zaben.
Daga karshe, Alkalin ya daga cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Oktoba domin bawa wadanda akayi kara damar shirya yadda za su kare kansu.

Post a Comment

0 Comments