Hotunan auren wani Bahaushe da Baturiya da su ka birge jama'a

Wani Bahaushe da ke zaune a birnin tarayya, Abuja, ya angonce da amaryar sa 'yar asalin kasar Turkiyya.
Bikin ya matukar kayatar da burge jama'a musamman abokan ango da su ka halarci bikin. Yayin bikin, an bukaci angon ya buga ganga tare da yin rawa kamar yadda al'adar kasar Turkiyya ta tanada.
Amarya da angon sun kasance cikin walwala da farinciki kamar yadda za a iya gani a hotunan su.
Bahaushe da Baturiya da su ka burge jama'a
Bahaushe da Baturiya sun burge jama'a
Hotunan auren wani Bahaushe da Baturiya
Sai dai majiyar 24blog ba ta bayyana ma ta sunan Bahaushen ba ko na matar sa, illa iya kai dai an tabbatar da cewar Bahaushen Najeriya ne kuma an yi bikin ne a Abuja.