Hong Kong-Zhuhai-Macau: Batutuwa biyar kan gadar China mafi tsada

LABARAI DAGA 24BLOG
Daga Lam Cho Wai
BBC Chinese
China na shirin bude "gadar da ta ratsa teku mafi tsawo a duniya" domin bunkasa tattalin arzikinta.
Gadar wadda tsawonta ya kai tsawon kilomita 55 za ta hada Hong Kong da Makau da kuma Zhuhai da ke mashigin ruwa na Pearl River Delta.
Shugaban China Xi Jinping ne ake sa ran zai bude gadar ranar Talata. Ziyararsa za ta kasance wata alamar karfafa gwuiwa a bangaren tattalin arziki a yankin a daidai lokacin da rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ke kara ta'azzara.
Masu sukar aikin sun ce gadar wadda aka kashe yuan biliyan 48 (dala biliyan 6.92) ba wani abu bane face asarar kudaden al'umma.
1. Dalilin da China ta gina gada mafi tsada
Gadar ta hada yankuna uku da ke gabar tekun kudancin kasar. Hulumomi a yankin na ganin wannan kokarin zai janyo karuwar hadewar bangarorin kasar.
Gadar na da bangarori daban-daban, inda wani bangaren na cikin ruwa ne wani kuma na saman ruwa. Karfen da aka yi amfani da shi a wajen gina wannan gadar na iya gina Eiffel Tower na Faransa 60.
Kafin gina wannan gadar, tafiya daga Zhuhai zuwa Hong Kong a mota kan dauki kimanin sa'a hudu - amma wannan sabuwar gadar ta mayar da nisan zuwa minti 30 kacal.
An shafe shekara tara ana gina gadar, kuma shugaban China na son samar da yani yanki da zai yi gasa da na Greater Bay Area da ke San Francisco da New York a Amurka da kuma na Tokyo.
Ana kuma ganin ziyarar da Xi Jinping ya kai manuniya ce ga yadda China ke kokarin bunkasa tattalin arzikin yankin.
2. Anya ba ta yi tsada ba kuwa?
An gina gadar a kan dala biliyan $6.92, bayan da aka sami jinkiri na shekaru biyu, wanda ya sa ta kara tsada na kimanin kashi 25 cikin 100 na kudin da aka shiry akashewa tun da farko.
Idan aka lissafta sauran ayyuka, yankin Hong Kong ya kashe dala biliyan 15 wajen aikin.
Masu sukar aikin sun ce asarar kudaden gwamnati ne kawai, kuma babu tabbacin za a sami bunkasar tattalin arziki.
3. Yaya batun ingancin gadar?
An gina gadar da shirin jure wa girgizar kasa da mahaukaciyar guguwa irin ta typhoon, kuma injiniĈ´oyi sun gina wasu tsibirai na musamman tsakanin Hong Kong da Macau.
Al'ummar Hong Kong sun nuna damuwa game da ingancin aikin bayan da aka sami wasu matsaloli. An tuhumi fiye da mutum 12 a kan cin hanci da rashawa bayan da aka gane cewa sun boye ainihin ingancin simintin da aka yi amfani da shi.
Hotunan da suka bayyana a shafukan intanet sun nuna wasu daga cikin bulo mai tare igiyar ruwa na yawo a cikin teku, lamarin da ya sa ake tsoron ko sun bi igiyar ruwa ne daga inda aka kafa su.
4. Ma'aikata 18 ne suka mutu
Kafofin watsa labarai na kiranta "gadar mutuwa".
Ma'aikata 18 ne suka rasa rayukansu, kuma daruruwa sun sami raunuka a yayin gina gadar, kamar yadda sashin harshen Sin na BBC ya bayyana.
Wasu daga cikinsu injina ne suka buge su, wasu kuma sun fada teku ne daga kololuwar gadar.
5. Tasirin ginin ga muhalli
Hukumomi sun ce sun yi "iya kokarinsu" domin kare muhallin yankin da ke kusa da gadar.
Amma wasu kungiyoyi sun musanta haka, inda suka ce aikin ginin gadar da ya hada da kwashe kasa a wurin aikin, abin da ake gani ka iya janyo kashe halittun da ke rayuwa a wurin.
Daya daga cikin halittun da lamarin ya shafa su ne na manyan kifayen nan da ake kira fararen dolphin - wadanda kawo yanzu ba a ganinsu.
Kungiyar IUCN mai samar da wani bayani na Red List mai duba halittun da ke kan hatsarin bacewa daga doron kasa ta ce suna "cikin hatsari matuka".
Yawan fararen kifayen dolphin da ake gani a gabar tekun Hong Kong sun ragu daga 148 zuwa 47 a cikin shekaru goma da suka gabata, kuma a yanzu ba a ganinsu a kusa da gadar, kamar yadda reshen kungiyar World Wide Fund for Nature.