Hadimin matar gwamnan Bauchi ya kwanta dama

LABARAI DAGA 24BLOG
Alhaji Bello Galadima, Hadimin uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar ya rasu.
Labaran rasuwarsa yana dauke cikin wata sanarwa ne da ta fito daga, Rashida Yusuf sakataren yadda labarai na uwargidan gwamnan.
Uwargidan gwamnan ta yi juyayin rasuwarsa inda ta bayyana cewar mutum ne mai aiki tukuru kuma ya gudanar da ayyukansa iya kokarinsa a lokacin da ya ke raye.
Hadimin matar gwamnan Bauchi ya kwanta dama
Hajiya Abubakar tayi addu'ar Allah ya jikansa, ya yafe kurakurensa ya kuma saka masa da gidan aljanna.
Ta bukaci iyalan mammacin su dauki rasuwarsa a matsayin kaddara daga Allah kuma tayi addu'ar Allah ya basu hakurin jure rashinsa.
Kafin rasuwarsa, marigayi Bello Galadima shine mataimakin na musamman kan tsare-tsare da hidimomi na Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar.
A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa kotun tarayya da ke Abuja ta bawa tsohon gwamna jihar Adamawa, Murtala Nyako izinin fita kasar Jamus domin likitoci su duba lafiyarsa.
Hukumar EFCC ne ta gurfanar da Nyako da yaransa bisa zarginsa da karkatar da kudin al'umma yayin da ya ke gwamna a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar lab