Gasar karatun Al-Kur'ani: Dan asalin jihar Katsina ya bayar da mamaki a Saudiyya

LABARAI DAGA 24BLOG
- Wani dan asalin jihar Katsina, Abdulganiyu Aliyu ya zo na uku a fagen gasar karatun Al-Qurani mai girma na duniya da aka gudanar a Saudiyya
- Abdulganiyu Aliyu da Ameer Yunus daga jihar Bauchi ne suka wakilci Najeriya a wajen gasar da aka yi a birnin Madina
- Mutane 115 daga kasashen duniya 82 ne suka fafata a gasar karatun Al-Quranin da aka kammala ranar Laraba da ta gabata
Gasar karatun Al-Kur'ani: Dan asalin jihar Katsina ya bayar da mamaki a Saudiyya
Wani dan asalin jihar Katsina da ya fito daga karamar hukumar Katsina, Abdulganiyu Aliyu ya yi nasarar zuwa na uku a gasar karatun Al-Qurani mai girma na kasa da kasa ta 2018 da akayi a kasar Saudiyya.
Abdulganiyu Aliyu ya fafata a gasar ne tare da sauran mallarta gasar guda 115 daga kasashe 82 na duniya.
shugaban jam'iyyar PDP a Gombe
Legit.ng ta samo wannan labarin ne ta dalilin shafin Leadership wata ta zanta da mai bawa gwamnan jihar Katsina shawara na musamman kan ilimi mai zurfi, Mallam Bishir Usman Ruwan Godiya wadda ya yiwa Aliyu rakiya zuwa wajen gasar.
Abdulganiyu Aliyu da kuma Ameer Yunus daga jihar Bauchi ne suka wakilci Najeriya a wajen gasar da aka gudanar a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Abdulganiyu Aliyu ya zo na uku a fannin hadar izihi 60 na gasar karatun Al-Qurani yayin da shi kuma Ameer Yunus ya zo na uku a bangaren hadar izihi 60 na Al-Qurani tare da tajawidi.
Kasar Saudiyya mai masaukin baki ita ce ta zo na farko sannan kasar Libiya da Najeriya suke biye da ita.
Wannan dai ba shine karo na farko ba da 'yan Najeriya ke nuna irin wannan bajinta a fagen gasar karatun Al-Qurani mai girma a fadin duniya ba.