Fayose: Kotu ta hana tsohon gwamnan Ekiti tafiye-tafiye

LABARAI DAGA 24BLOG
Wata babbar kotu a birnin Legas ta ba tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose beli, inda ta hana shi tafiye-tafiye.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ce ta shigar da kara a kotun, inda take neman a hukunta shi saboda ta ce ya karbi dala miliyan biyar daga hannun tsohon ministan tsaro, Musiliu Obanikoro, wadanda ya yi amfani da su wajen yakin neman zabe don zama gwamnan Ekiti a shekarar 2014.
Hukumar ta kuma shigar da wasu kararraki 10 bayan wannan.
Amma kotun ta gindaya wa tsohon gwamnan wasu sharudda kafin ta amince da ba da belinsa:
Zai mika takardar lamuni ta banki ta naira miliyan 50
Zai mika fasfonsa
Zai kai mutum biyu da za su tsaya masa
Sannan zai mika takardun shaidar biyan haraji na shekara biyu
Kakakin Mista Fayose, Lere Olayimika, ya ce za su tabbatar sun mika dukkan abubuwan da kotun ta bukata nan ba da jimawa ba.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.
Mista Fayose ya musanta cewa ya aikata laifukan da hukumar EFCC ta kai shi kara a kansu.
Amma tsohon gwamnan ya ce ranar Juma'ar da ta gabata ce ya fara jin cewa za a maka shi a wata kotu a Legas.
Wannan dalilin ne yas a ya umarci lauyansa da ya nemi a ba da belinsa, kuma alkalin kotun ya ce Fayosen na iya neman beli kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Fayose: Make Nigerians no mind EFCC…and kontinu to ask why dem never charge Fayose go court since dem claim say dem get...
Posted by BBC News Pidgin on Monday, 22 October 2018
Tshohon gwamnan na Ekiti ya kuma zargi hukumar EFCC a shafinsa na Twitter, da bata lokaci wajen gudanar da shari'ar, bayan da ya ce sun yi ta kurarin suna da kwararan shaidu cewa ya aikata laifukan da ta ke tuhumarsa da aikatawa.
Amma bayan kwana biyu kacal, sai hukumar ta EFCC ta maka shi a kotu a ranar Litinin 22 ga watan Oktoba, inda ta tuhume shi da aikata laifuka 11.
Hukumar ta ce tsohon gwamnan na da hannu cikin aikata laifukan karkatar da kudin gwamnati a lokacin zaben 2014 da kuma lokacin da yake rike da mukamin gwamna a karo na biyu.
Wasu daga cikin tuhume-tuhume sun hada da:
Tuhuma ta farko: Ya karbi haramtattun kudade da suka kai Naira 1,219,000,000 (Biliyan daya da miliyan dari biyu da 19) da ya yi amfani da su wajen gudanar da yakin neman zabensa na zama gwamna a watan June, 2014
Tuhuma ta 2: Cewa ya karbi dalar Amurka 5,000,000 (miliyan biyar) daga hannun tsohon ministan tsaro Sanata Musiliu Obanikoro a watan Yuni na 2014
Tuhuma ta 3: Ya ajiye Naira 300,000,000 (miliyan dari uku) a wani asusun ajiya, wanda ya saba wa dokar Najeriya
Tuhuma ta 4: Sannan kamfaninsa mai suna Spotless Limited tare da wasu 'yan gidansa suna juya haramtatun kudade da yawansu ya kai N317,000,000 (Naira miliyan dari uku da goma sha bakwai)
Wannan ba karamin koma baya ba ne ga Mista Fayose, wanda a makon jiya shi ne gwamnan jihar Ekiti, kafin ya sauka ya mika wa sabon gwamna Kayode Fayemi mukamin.
Kuma shi ne gwamna na karshe dan jam'iyyar PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wanda ya dade yana adawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.