Online counter

Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'

Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'

LABARAI DAGA 24BLOG
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Lahadi da ta gabata ta ce yanzu dai kam gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya tabbatar wa da duniya cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), taron mayaudara ne kawai.
A jiya ne dai gwamnan na Legas ya kira wani taron manema labarai na kasa-da-kasa inda ya bayyana abokin hamayyar sa a zaben fitar da gwani da jam'iyyar zata gudanar a jihar Babajide Sanwo-Olu a matsayin tsohon dan damfara kuma mai tabin hankali.
gwamnan na jihar Legas yanzu haka yana fuskantar matsala bayan da ya shiga tsaka mai wuya biyo bayan sabanin da ya samu da jagoran jam'iyyar APC a jihar Cif Bola Tinubu.
Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP Mista Kola Ologbondiyan ya kara da cewa duba da irin hakan ne yake kara kira da 'yan jam'iyyar da ma sauran 'yan Najeriya da su guji jam'iyyar a zabukan 2019 masu zuwa.
A wani labarin kuma, Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta ce abun kunya ne a ce jam'iyyar tana a cikin aljihun mutum daya kuma wannan mutumin ya kasance shine Gwamnan jihar Ribas Mista Nyeson Wike.
Jam'iyyar ta cigaba da cewa kawo yanzu dai dukkan duniya ta tabbatar da cewa gwamnan na Ribas shine shugaban jam'iyyar ta PDP sannan kuma shine mai magana da yawun ta.

Post a comment

0 Comments