Da dumin sa: Sheikh Gumi ya yi magana game da rikicin Kaduna

LABARAI DAGA 24BLOG
- Sheikh Gumi ya yi magana game da rikicin Kaduna
- Ya shawarci mutane su zauna lafiya
- Ya ce ya kamata gwamnati ta samarwa matasa da abun yi
Fitaccen malamin addinin nan na Islama kuma masanin tafsirin Al-qur'ani mai girma, Dakta Ahmad Gumi yayi tsokaci game da rikicin da yanzu haka yaki ci ya ki cinyewa a jihar Kaduna inda yayi kira ga dukkan bangarori da su zauna da juna lafiya.
Da dumin sa: Sheikh Gumi ya yi magana game da rikicin Kaduna
Dakta Gumi dai yayi wannan tsokacin ne a lokacin da yake zantawa da wakilin majiyar mu na jaridar Daily Trust biyo bayan sake saka dokar tabacin awa 24 da gwamnatin jihar ta sake sawa.
Samu cewa haka zalika shahararren malamin ya kuma roki al'umma musamman ma matasa da su daure su nemi sana'a tare da kira ga gwamnati da ta samarwa al'ummar ta yanayi mai kyau na san'ar domin samun dawwamammen zaman lafiya.
Da safiyar ranar Juma'a ne dai gwamnatin jihar ta Kaduna ta sake kakaba dokar ta-baci ta awa 24 biyo bayan sake bullar wata sabuwar tarzomar.