Buhari ya bayyana babban taimakon da Afirka ke nema daga Kasashen Turai

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban taimakon da kasahen Turai da Amurka za suyi wa Afirka shine taimakawa nahiyar ta janyo ruwa zuwa tafkin Chadi.
Shugaban kasan ya fadi hakan ne a yau Juma'a a gidan gwamnati inda ya karbi bakuncin Ciyaman din Kungiyar Hadin kan kasashen Afirka, Moussa Mahamat.
Shugaba Buhari ya ce tafkin na Chadi da ke samar wa miliyoyin mutane daga kasashen Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya sana'o'i yana fuskantar barazanar kafewa saboda matsalar dumamar yanayi.
Buhari ya bayyana babban taimakon da Afirka ke nema daga Kasashen Turai
"Mutane da yawa da ke kamun kifi, noma, kiwo da wasu sana'o'in sun shiga tsaka mai wuya. Wannan yana daga cikin dalilan da yasa matasa daga Afirka ke bin Sahara ko Teku domin haurawa kasashen Turai amma taimakawa a janyo ruwa zuwa tafkin zai rage matsalar, " inji Buhari.
Shugaba Buhari ya kuma ce Najeriya za ta cigaba da sauke nauyin da kungiyar da Tarayyar Kasashen Afirka a daura mata duk da irin nauyin da ke kanta saboda yawan al'umma da ma'adanai da kasar ke da dashi.
Mr Mahamat ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari saboda irin shugabancin da ya ke yi a Najeriya da ma Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka.
Ya kara da cewa AU za ta mayar da hankali kan yadda Afirka za tayi hadin kai da sauran kasashe duniya musamman ta fannin tafiye-tafiye, kasuwanci da ma wasu muhimman abubuwan.