Online counter

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 4 da suka turo Najeriya

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 4 da suka turo Najeriya

LABARAI DAGA 24BLOG
Buhari ya karbi bakoncin jakadun ne a ranar Talata 16 ga watan Oktoba a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja, inda jakadun kasashen Japan, Rasha, UAE da Brazil suka mika masa shaidar nadasu wannan mukami.
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya

Jakadun sun hada da Yutaka Kikuta daga kasar Japan, Alexey Shebarsin daga kasar Rasha, Richardo Guerra DE Araujo daga kasar Brazil, sai kuma Fahad Obaid Mohammed Obaid Altaffag daga kasar UAE Dubai.
A wani labarin kuma fadar shugaban kasa ta musanta rahoton dake yawo na cewa wai gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hana wasu manyan mutane guda hamsin ficewa daga Najeriya saboda tuhume tuhumen da take musu da suka shafi cin hanci da rashawa.
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba, don yin bayani dalla dalla game da sunayen da wata jarida ta buga na cewa sune mutanen da gwamnati ta yi ma wannan takunkumi.
“Ina tabbatar muku babu wani jerin sunayen mutane da aka hana fita, kuma bamu muka fitar da sunayen ba, yawancin sunayen da aka ambata sunaye ne da an san da maganan shari’unsu, don haka fitar da sunayensu ko akasin haka ba zai kara musu nauyi laifi ba.” Inji shi.
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya

Amma Malam Garba yayi Karin haske game da sabuwar dokar da gwamnati ta samar ‘EO 6’
“Dokar EO 6 za ta sauya fasalin yaki da rashawa a Najeriya, manufarta itace don kara sauri ga shari’un da ake yi da suka shafi yaki da rashawa, tare da rage adadin lokacin da ake dauka ana gudanar da shariar.” Inji shi

Post a Comment

0 Comments