Bayan sulhun: Obasanjo ya shiga gaba wajen ganin Amurka ta yafewa Atiku

LABARAI DAGA 24BLOG
- Obasanjo ya shiga gaba wajen ganin Amurka ta yafewa Atiku
- Jam'iyyar APC ce tayi wannan zargin
- Amurka dai ta hana Atiku Abubakar zuwa kasar ta
Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta zargi tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da shiga gaba tare da yin kutun-kutun wajen ganin kasar Amurka ta yafewa tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar laifin sa.
Bayan sulhun: Obasanjo ya shiga gaba wajen ganin Amurka ta yafewa Atiku
Jam'iyyar ta APC ta ce ta samu wannan bayanan ne na sirri daga wasu makusantan na tsohon shugaban kasar wanda a ranar Larabar da ta gabata ne suka yi sulhu da mataimakin nasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zaben 2019 mai zuwa.
 Wannan dai ikirarin na jam'iyyar ta APC na kunshe ne a cikin wata sanarwar da maimagana da yawun ta Mista Yekini Nabena ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai.
Shi dai Atiku Abubakar ance kasar ta Amurka yanzu haka ta saka shi a cikin jerin masu laifi tun bayan da ta zarge shi da hannu dumu-dumu a wata almundaha na kudade a shekarar 2005 lokacin yana mataimakin shugaban kasa.