Online counter

Bayan bincike, Jami'a ta kori sabbin Farfesoshi har biyu saboda iskanci da mata

Bayan bincike, Jami'a ta kori sabbin Farfesoshi har biyu saboda iskanci da mata

LABARAI DAGA 24BLOG
Hukumar ladaftarwa ta jami'ar jihar Legas ta amince da korar malaman ta guda uku sakamakon lalata da dalibai tare da rashin da'a.
Kwamitin ta yanke hukuncin ne a taron ta na 119 da tayi a ranar Alhamis, 4 ga watan Octoba. Malaman da aka kora sun hada da : Dr. Adubunmi Ayoola Sunkanmi, mai neman zama farfesa a bangaren tattali na jami'ar ; Dr. Ogunwande Isiaka Ajani, mai neman zama farfesa a bangaren Chemistry da Dr. Gbeleyi Emmanuel Orilade, malami a mataki na biyu a bangaren Anatomy.
Kwamitin ta amince da karawa malamai masu koyarwa 49 da malamai 200 marasa koyarwa zuwa matsayi daban daban.
Hukuncin da hukumar ladaftarwa ta jami'ar ta nuna cewa bazata amince da lalata da dalibai ba da kuma rashin da'a tare da cigaba tabbatar da walwalar malaman da yakamata da dalibai a jami'ar.

Post a comment

0 Comments